An harbe lauyan gwamnati a Iran

Iyakar Iran da Pakistan
Image caption Iyakar Iran da Pakistan

Rahotanni daga Iran na cewa an harbe wani lauyan gwamnati har lahira a lardin Sistan-Baluchistan da ke daura da iyakar kasar da Afghanistan da Pakistan.

An kashe shi ne tare da direbansa a lokacin da yake tafiya aiki a garin Zabol.

Harin na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan da 'yan bindiga suka kashe jami'an tsaron iyaka 14 a lardin, kuma mahukunta suka rataye fursunoni 16 a matsayin fansa.

Yankin iyakar gabashin Iran dai na fama da 'yan tawaye daga bangaren Muslim 'yan sunna marasa rinjaye da kuma masu fataucin kwayoyi.