Jonathan na neman karin wa'adin dokar ta baci

Sojojin Nigeria sun mamaye arewa maso gabashin kasar sanadiyyar dokar ta baci
Image caption Sojojin Nigeria sun mamaye arewa maso gabashin kasar sanadiyyar dokar ta baci

Shugaban kasar Nigeria Goodluck Jonathan ya nemi izinin majalisar dokoki kan kara wa'adin dokar ta baci a jihohi uku da ke arewa maso gabashin kasar da ke fama da 'yan bindiga masu kishin Islama.

Mr. Jonathan ya bukaci haka ne cikin wata wasika da ya aikewa majalisar wakilan kasar a ranar Laraba.

Ranar 14 ga Mayun bana ne dai shugaban ya kafa dokar ta baci a jihohin Yobe, Adamawa, da Borno tushen kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna lid da'awati wal jihad, da ake kira Boko Haram, wacce mayakanta suka kashe daruruwan jami'an tsaro da fararen hula.

Dubunnan sojoji da 'yansandan da aka kai yankin sun kori mayakan kungiyar daga cikin manyan birane amma dai ba su kai ga murkushe su dungurungum ba.