Netanyahu ya zargi Palasdinawa

Image caption Kerry da Netanyahu

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya zargi Palasdinawa da haddasa tashe tashen hankali na ba gaira ba saba.

Ya bayyana haka ne a lokacin ziyarar da sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya soma a yankin don farfado da tattaunawar zaman lafiyar da aka dakatar.

Palasdinawan da ake tattaunawa da su sun yi kurarin ficewa daga tattaunawar sabili da gine-ginen da Isra'ila ke yi a gabar yammacin kogin Jordan da ta mamaye.

Lokacin ziyararsa ta baya bayannan a yankin, Mr Kerry ya tattauna da Mr Netanyahu a Jerusalem, yanzu haka kuma ya na Bethlehem in da zai gana da shugaban Palasdinawa, Mahmud Abbas.

Karin bayani