Man United ta yi canjaras da Sociedad

Karon Man united da Real Sociedad
Image caption Karon Man united da Real Sociedad

Manchester United na cigaba da jagorar rukunin da ta ke ciki a gasar Zakarun Turai, duk da barar da fenariti da Robin van Persie ya yi, abinda ya hana kungiyar samun nasara a gidan Real Sociedad.

Bayan da ta doke Sociedad a karonsu na farko,da canjaras din da aka yi tsakanin Shakhtar Donetsk da Bayer Leverkusen, wannan rashin nasara za ta iya yiwa Man United cikas a yunkurinta na isa mataki na gaba.

Kawo yanzu dai su ne kan gaba a rukuninsu, da tazarar mako tsakaninta da Leverkusen, kuma idan United ta samu nasara kan Jamusawan a wasansu na ranar 27 ga Nuwamba, za ta fito daga rukuninta.