Ban Ki-moon ya kammala ziyara a Nijar

Mr Ban Ki-moon
Image caption Mr Ban yana jagorantar wata muhimmiyar tawaga

A jamhuriyar Nijar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon wanda ke wani rangadi a yankin Sahel, ya kammala ziyarar aikin da ya kai kasar.

Mr Ban, ya ce Majalisar Dinkin Duniyar tare da Bankin duniya da kungiyar Tarayyar Turai sun amince su tallafa ma kasashen yankin na sahel da ke fuskantar kalubale iri- iri da kudade domin inganta tsaro da ayyukan ci gaba mai dorewa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar, ya kuma ziyarci wani asibitin kula da kananan yara dake Yamai, sannan ya yi wani jawabi ga majalisar dokokin kasar ta Nijar.

Mr Ban, wanda tuni ya ziyarci kasar Mali, yana jagorantar wata muhimmiyar tawaga ce da ta hada da shugaban bankin duniya da na bankin raya kasashen Afruka da na Tarayyar Turai da kuma shugabar Hukumar Tarayyar Afruka.

Da Yamma ne Mr Ban din ya tashi daga birnin Yamai domin zuwa Burkina Faso, kuma zai kitse rangandi nasa ne da kasar Cadi.

Karin bayani