Shell na yin karya kan malalar mai

Malalar mai na illa ga yankin Niger Delta
Image caption Malalar mai na illa ga yankin Niger Delta

Kamfanin man fetur na Shell na ba da bayanan karya game da malalar mai a Nigeria in ji kungiyar Amnesty International da cibiyar kare hakkin muhalli ta CEHRD.

Wani rahoto da ka wallafa a yau ya bankado lokuta da dama da Shell ya ba da bayanan karya game da sababin malalar mai, adadin man da ya malala da kuma aikin da aka yi na tsaftace muhallin.

Rahoton ya ce tsarin da ake bi wurin gano dalili da yawan malalar mai a Nigeria na da matukar rauni.

Tasirin hakan kan al'umomin da abin yake shafa shi ne karanci ko ma rashin diyya dungurungum.

Kungiyoyin Amnesty International da CEHRD sun bukaci wani kwararren mai binciken malalar mai da ke zaman kansa a Amurka ya yi nazarin rahotannin da kamfanonin man fetur a yankin Niger Delta da kuma gwamnatin Nigeria ke fitarwa game da malalar mai a yankin.

'Ba sata ba ce'

Image caption Yadda mai ya lahanta muhalli

Kwararren ya gano cewa ana yawan danganta malalar man da aikin barayin fetur bayan a mafi yawan lokuta rashin ingancin kayan aiki ne ke haddasa hakan.

Wannan na faruwa ne saboda hukumar kula da malalar man fetur ta Nigeria ba ta da kwarewa da wadatar kayan aikin da za ta gudanar da binciken sai dai ta dogara akan kamfanonin fetur din su sanar da ita abinda su ka gano.

Malalar man fetur dai ta zama ruwan dare a Nigeria inda take mummunar barna ga muhalli, tabarbarar da tattalin arziki da kuma jefa rayukan al'umma cikin hatsari.

Abubuwan da ke jawo malalar mai sun hada da tsatsa, rashin kula da bututun jigilar mai, rashin ingancin kayan aiki da kuma satar man fetur.

Kamfanin Shell ya sha nanatawa masu zuba jari, abokanan hulda, da kafafen yada labarai cewa sata ce tafi komai janyo malalar mai. Sai dai hujjojin da masu binciken su tattara sun nuna ba haka bane.

Image caption Ana yawan zanga zanga a kan Shell

Kungiyoyin Amnesty International da CEHRD na kira ga dukkan kamfanonin fetur da su bayyana cikakkun rahotannin binciken da su kan yi, tare da hotuna da bidiyo domin tantance gaskiyar me ke faruwa.

Haka kuma kungiyoyin sun bukaci gwamnatin Nigeria da ta karfafa gwiwar hukumar da ke kula da malalar mai ta hanyar kara mata kaso cikin kasafin kudin kasa.

A martaninsa, kakakin kamfanin Shell ya karyata zarge-zargen, inda yace an kambama batun fiye da kima a kan malalar danyen mai.

A cewarsa, kamfanin na kokarin bullo da wasu karin hanyoyin magance matsalar da kuma sa'ido sosai a kan batun malalar mai don samun hanyoyin inganta rage barnar da mai kanyi a yankin.