Adamawa ta yi watsi da karin dokar-ta-baci

Gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa
Image caption Gwamna Murtala Nyako na jihar Adamawa

Gwamnatin jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Nigeria ta bukaci majalisar dokokin kasar kar ta amince da kudirin kara wa'adin dokar-ta-bacin a yankin.

Ranar Laraba shugaban kasa Goodluck Jonathan ya aikewa da majalisar dokokin bukatar kara wa'adin dokar-ta-bacin a jihohin Borno, Yobe da Adamawa na tsawon watanni shida.

Sai dai kakakin gwamnatin jihar Adamawa Ahmed Sajo yace bai ga dalilin da za'a sa Adamawa cikin jerin jihohin da aka kakabawa dokar-ta-bacin ba.

A cewarsa idan har an sa Adamawa cikin jihohin ne saboda gudun kar mayakan Jama'atu Ahlis sunnah lidda'awati wal jihad su gangara jihar idan an koro su daga sansanoninsu da ke Borno da Yobe, don me ba'a sa jihohin Bauchi da Gombe masu makwabtaka ba?