Mourinho ya hukunta Hazard kan lattin atisaye

Eden Hazard
Image caption Eden Hazard

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce ya cire Eden Hazard daga tawagar 'yan wasansa da suka casa Schalke 3-0 ne saboda ya yi lattin halartar filin atisaye.

Mourinho ya canja yan wasa shida, har da Harzard, bayanda ya ce ya yi "kurakure 11" a karawar da Newcastle ta casa su da ci 2-0 ranar Asabar.

Kocin ya ce "ba zanyi karya ba, bai gamu da rauni ba, ya manta da lokacin atisaye ne. Yaro ne karami, kuma yara kan yi kurakure sai dai iyaye su yi kokarin fadakar su."

Mourinho ya ce rawar da 'yan kwallonsa suka taka ta nuna farfadowarsu daga rashin nasarar da suka samu a Newcastle. Ya kara da cewa dan kwallon na Belgium mai shekaru 22 "bai ji dadi da ban sashi a wasan ba, domin yaso ya buga kwallo."