Za a cimma yarjejeniya kan nukiliyar Iran

Cibiyar nukiliya ta Iran
Image caption Cibiyar nukiliya ta Iran

Ministan harkokin waje na Iran Javad Zarif ya bayyana yiwuwar cimma wata yarjejeniya a tattaunawar da za'a yi ranar Alhamis game da shirin nukiliyar kasar.

Javad Zarif ya ce za'a sha tata-burza a tattaunawar amma dai ya na fatan warware rashin aminci da ke tsakaninsu da kasashen Yammancin duniya.

Kasashen Yamma dai na zargin Iran na kokarin kera makaman nukiliya ne.

Sai dai gwamnatin Iran ta ce ta na binciken nukiliya ne domin samar da makamashi ba makamai ba.

Kasashen Yamma na sa ran Iran za ta dakatar da duk wani shiri da ta ke nukilya, inda su kuma za su janye wasu daga cikin takunkumin da suka kakabawa kasar kafin lokacin da za'a warware batun baki daya.

Tun bayan da sabon shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya dare mulki a watan Agusta aka fara samun fahimtar juna tsakanin kasar da kasashen Yamma.