Zargin cin hanci a Majalisar dokokin Kaduna

Mukhtar Ramalan Yaro
Image caption Ana zargin wasu 'yan majalisar Kaduna sun karbi miliyoyi

Majalisar dokokin jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta bukaci a gudanar da cikakken bincike a bisa zargin bai wa wasu daga cikin 'yan majalisar cin hancin naira miliyan 10 don goyon bayan tsige kakakin majalisar Alh Usman Gangara.

Majalisar ta bukaci a gudanar da wannan bincike ne bayan da ake ci gaba da zargin 'yan majalisar da karbar cin hancin Naira Miliyan 180, da aka rabawa wadanda suka goyi bayan tsige Alh Usman Gangara da sauran shugabannin majalisar da a yanzu ke kalubalantar tsige sun a kotu.

Wasu daga cikin 'yan majalisar dai na nuna damuwa a bisa wannan zargi wanda suka ce ya taba mutuncin majalisar.

Gwamnatin jihar Kaduna dai har yanzu ba ta ce komai ba game da wannan batu.

Karin bayani