Kotun Turai ta goyi bayan 'yan luwadin Afrika

'Yan luwadi da madigo na fuskantar tsangwama a Afirka
Image caption 'Yan luwadi da madigo na fuskantar tsangwama a Afirka

Kotun tarayyar turai ta yanke hukuncin cewa yan Luwadi da madigo da ke fuskantar hadari na matsanancin hukunci da cin zarafi a karkashin dokokin kasashensu na asali na da hurumin neman mafakar siyasa a kasashen kungiyar Tarayyar Turai.

Kasar Netherlands ce ta bukaci kotun ta fayyace mata ko za'a iya sanya wasu 'yan Luwadi su uku yan kasashen Salio da Uganda da kuma Senegal cikin jerin mutanen dake fuskantar matsanin cin zarafi a kasashensu.

Kotun ta yanke hukuncin cewa ana iya basu mafaka. Kasashe da dama dai a Afirka sun haramta aikata Luwadi.