Kwamandoji M23 sun mika wuya a Uganda

Image caption Sultani Makenga

Jami'ai a kasar Uganda sun ce kwamandojin soji na kungiyar 'yan tawayen M23 wadanda aka ci da yaki sun mika kansu ga hukumomin Ugandan.

An ruwaito cewa daruruwan mayakan sun yi saranda tare da shugabansu Sultani Makenga.

Sun mika kansu ne ga sojojin Uganda a gandun dajin Mgahinga dake kan iyaka tsakanin Uganda da Jamhuriyar dimokradiyyar Congo.

A ranar Talata kungiyar M23 ta sanar da kawo karshen tawaye a gabashin Congo bayan da sojojin gwamnati dake samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya suka fatattakesu daga sansanonin da suka yi kakagida.

Karin bayani