'Yan Nijar na maida martani ga Ban Ki Moon

Mata a Nijar kan haifi 'ya'ya da yawa
Image caption Mata a Nijar kan haifi 'ya'ya da yawa

A Jamhuriyar Nijar, wasu al'ummomin kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu dangane da kiran da Babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya yi ga al'ummomin dake yankin Sahel da su rungumi tsarin takaita iyali.

Babban Sakataren na majalisar dinkin duniya ya ce hakan zai taimaka wajen rage irin wahalhalun rayuwa da ake fuskanta a yankin.

A lokacin da yake kammala ziyararsa a kasar, Mr Ban Ki Moon ya lura da cewa daukar wannan mataki zai taimaka wajen baiwa hukumomi sukunin aiwatar da abubuwan more rayuwar al'ummar.

Sai dai wasu 'yan kasar na ganin cewa hakan duka ya danganta ne da karfin mutum.

Malaman addinan musulunci dana Kirista a jamhuriyar Nijar ma suna da ra'ayoyi mabanbanta game da wannan batu.

Karin bayani