Fazlullah ya zama sabon shugaban Taliban

Image caption Fazlullah ya sha alwashin yin ramuwar gayya

Kungiyar Taliban reshen kasar Pakistani ta bayyana cewa ta zabi Mullah Fazlullaha matsayin sabon shugabanta.

Magoya bayan Fazlullaha ne dai suka dauki alhakin harbin yarinyar nan 'yar makaranta, Malala Yousufzai.

'Yan kungiyar sun kara da cewa Fazlullaha ya yi watsi da tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar, kuma yana so ya dauki fansar kisan da aka yi wa mutumin da ya gada, Hakimullah Mehsud, a harin da aka kai da jirgin samar Amurka maras matuki ranar Juma'a.

Wani kakakin Taliban ya shaidawa BBC cewa za su rika kai hare-hare kan sojoji da 'yan jami'yar da ke mulkin kasar.

Fazlullaha ya shahara ne shekaru 6 da suka gabata lokacin da dakarun da yake marawa baya suka kwace ikon yankin Swat da ke arewa maso yammacin Pakistan, inda mutane ke bin tsarin Sharia'ar musulinci.

Karin bayani