An sace wani attajiri a jihar Sokoto

Image caption Alhaji Abu Dankure

'Yan sanda a jihar Sakkwato dake arewacin Nigeria sun soma farautar wasu 'yan bindiga da suka yi awon gaba da wani attajiri a jihar.

Shaidu sun shaidawa BBC cewar 'yan bindigar sun sace Alhaji Abu Dankure ne yana cikin motarsa a daren ranar Laraba.

Mai magana yawun 'yan sanda a jihar Sakkwato, DSP Al-Mustapha Sani ya bayyanawa BBC cewar jami'ansu na aiki domin gano inda ake tsare wannan dattijon kuma tuni har sun gano motarsa a Durbawa, wani gari dake wajen birnin na Sakkwato.

Alhaji Awwalu Illa wanda yayi magana da yawun iyalan wanda aka sacen, yace har Yanzu ba su samu wani Labari game da shi ba.

Karin bayani