Darajar Twitter ta haura dala biliyan 25

Twitter a kasuwar kudaden New York
Image caption Twitter a kasuwar kudaden New York

Darajar hannun jari a shafin blog na Twitter ta kusan ninkawa biyu a sa'oin farko na hada hada a kasuwar hannun jarin New York.

Farashin hannun jarin ya daga sama da dala arba'in da biyar, wanda ya kai darajar kamfanin sama da dala biliyan ashirin da biyar.

In ji wakilin BBC Mark Gregory, kamar abin da ya faru ne da hannun jarin Facebook, inda kwanaki kadan kafin sayar da shi aka yi ta rububin nemansa, sai suka kara darajarsa, suka kuma kara yawan hannayen jarin.

Shafin Blog din na Twitter yana daya daga cikin shafukan sada zumunta da suka fi tashe.

Yana da mutane fiye da miliyan dari biyu wadanda ke aikewa da sakon Tweet miliyan dari biyar a kowace rana.

To sai dai bai kai ga samun riba ba tukuna.