Twitter zai sayar da hannun jari

shafin Twitter a kasuwar hannun jari ta New York
Image caption Cinikin shi ne na hannun jarin da aka fi zakuwa a gabatar da shi a kasuwa a shekaran nan

Kamfanin shafin sadarwa ta intanet na Twitter ya sanya farashin dala 26 kan hannun jarin da zai sayar ga jama'a.

Farashin dai ya dara yadda aka yi tsammani, kuma hakan na nufin darajar shafin na Twitter ta kai dala miliyan dubu 18.

A ranar Alhamis din nan ne za a fara sayar da hannun jarin na Twitter wanda daya ne daga cikin shafukan sadarwa na intanet da ke bunkasa cikin hanzari.

Sama da mutane miliyan 200 ne ke amfani da shafin, inda suke tura sakonni miliyan 500 a kowacce rana daya.