Shawarar Brazil da Jamus kan satar bayanai

Obama, da Rossef da Merkel
Image caption Majalisar Dinkin duniya za ta duba wanann shawara da kasashen suka gabatar

Brazil da Jamus sun gabatar wa Majalisar Dinkin Duniya wata shawara inda suke kira ga dukkanin kasashe su tabbatar da tsaro a kan harkokin intanet da na sauran sadarwa.

Kasashen sun dauki wannan mataki ne saboda zargin da a ka yi cewa hukumar tsaron cikin gida ta Amurka ta rika satar bayanan sadarwar shugabar kasar Brazil Dilma Roussef da na shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da kuma wasu karin bayanai.

Jakadan Brazil a Majalisar Dinkin Duniyar, Antonio Patriota ya ce idan dai har babu 'yancin sirri to ba lalle ba ne a samu ingantacciyar dumokradiyya a duniya.