An killace matar Gwamnan Enugu a cikin gida

Nigeria
Image caption 'Matar Gwamnan Enugu na bukatar taimako'

A Najeriya, jami'an hukumar kare hakkin bil-adama ta kasar , sun ce sun gana da matar gwamnan jihar Enugu, Mrs Clara Chime a fadar gwamnatin jihar, inda suka tarar ba ta da koshin lafiya, kuma tana bukatar karin taimako.

Halin da matar gwamnan ke ciki dai ya jawo cacar-baki, yayin da fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare hakkin bil'Adama da ke Legas, Femi Falana yake cewa an tsare wannan mata ba bisa ka'ida ba, shi kuma mijinta wato gwamnan na Enugu yake musanta hakan.

Babbar jami’ar ofishin hukumar kare hakkin bil-adama ta kasa a shiyyar kudu maso gabashin Najeriya Barista Uche Nwokocha, ita ce ta jagoranci wasu jami’an hukumar da suka ziyarci mai dakin gwamnan jihar Enugun, Mrs Clara Chime.

Jami'ar ta shaidawa BBC cewa ''Mun gan ta, mun zanta da ita da likitanta da yayyenta maza. Kuma ita ma kanta ta tabbatar mana, cewa tana fama da abin da ta kira ciwon bakin ciki, wanda kuma wani lokaci yake kai ta ga fama da ciwon jiye-jiye da gane marasa kan gado''.

Karin bayani