An kama jirgin Saliyo makare da makamai a Girka

Tutar Saliyo
Image caption 'Ana binciken inda jirgin zai nufa'

Jami'an tsaron bakin teku na kasar Girka sun kama wani jirgin ruwa mai dauke da tutar kasar Saliyo da aka gano yana dauke da tarin bundugogi da harsasai.

An tasa jirgin mai suna Nour M zuwa tashar jiragen rwa ta Rhodes ta kasar ta Girka bayan da ma'aikatansa suka kasa ba da takardun gaskiya game da kayan da yake dauke da su, ciki har da takardar majalisar dinkin duniya ta izinin safarar makamai a yankunan da ake rikici.

Jami'an tsaron bakin tekun na Girka sun ce suna kokarin gano inda jirgin wanda ya taso daga Ukraine zai je.