'Yan bindiga sun fafata a Tripoli

'yan bindiga a Libya
Image caption Fada tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Libya abu ne da ke aukuwa a lokaci zuwa lokaci

An yi ta jin karan bundugogin kakkabo jiragen sama da fashewar gurneti gurneti a sassa daban daban na babban birnin Libya Tripoli.

Wani jami'i a ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar, ya sheda wa BBC cewa dauki ba dadi ne a ka yi tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga biyu da ke adawa da junansu.

Kuma daya daga cikinsu tana da kusanci da ma'aikatar harkokin cikin gidan ta Libya.

An zarge ta ne da kashe wani mutum dan Misrata ranar Litinin, a don haka ne daya kungiyar ta kai mata hari domin daukar fansa.