Nijar da Benin za su gina hanyar jirgin Kasa

Shugaba Yayi Boni
Image caption Hanyar za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arziki

A jamhuriyar Nijar Shugaban Kasar Alhaji Mahamadu Isufou da takwaransa na Kasar Benin Dr Bony Yayi sun sa hannu a kan wata yarjejeniyar gina hanyar jirgin kasa da za ta hada Cotonou da Yamai.

Wannan hanyar za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da kyautata mu'amula tsakanin kasashen biyu.

A karshen watan Maris na 2014 ne ake sa ran soma aikin.

Shugabannin kasashen na Nijar da Benin sun cim ma sa hannu a kan yarjejeniyar ne yayin wata ziyarar aiki da shugaban na Nijar Alhaji Mahamadu Isufou ya kai kasar ta Benin a jiya.

Karin bayani