Yunkurin kafa doka kan malalar mai a Nigeria

Image caption Yadda mai ke barnata gonaki a Niger Delta

'Yan Majalisar dokokin Nigeria na tunanin kafa wata doka don cin tarar kamfanonin dake janyo malalar mai a kasar.

Matakin 'yan majalisar zai tilastawa kamfanonin mai na kasashen waje biyan miliyoyin daloli a duk shekara a matsayin tara.

Shugaban kwamitin kula da muhalli na majalisar dittajai, Sanata Bukola Saraki ya ce idan aka kafa dokar za ta janyo raguwa wajen lalata muhallin da kamfanonin mai kan yi.

Yanzu haka dai a duk shekara ana samun malalar mai a yankin Niger Delta sakamakon fashewar bututan mai.

A farkon wannan makonne, kungiyar Amnesty International ta soki kamfani Shell a kan yin coge game da batun malalar mai, amma kamfanin ya musanta zargin.

Karin bayani