Palasdinawa na zargin Isra'ila da kashe Arafat

Image caption Margayi Yasser Arafat

Hukumomin Palasdinu sun ce Isra'ila ce kadai suke zargi da hannu wajen kashe jagoransu Yasser Arafat, bayan wani rahoto daga Switzerland ya nuna cewar akwai gubar polonium a gawarsa.

Shugaban kwamitin Palasdinawa da ya bincike rasuwar Arafat a shekara ta 2004, ya bayyan mutuwar a matsayin 'kisan gilla'.

Ya ce za su ci gaba da bincike don tabbatar da bayanai game da mutuwar.

Isra'ila ta sha karyata zargin hannu wajen kisan Arafat.

Matar Arafat, Suha, ta ce wannan rahoton ya tabbarda kisan gilla aka yi masa, amma ta ce mijinta na da makiya a duniya, ba za ta iya cewa ga mai hannu a kashe shi ba.

Yasser Arafat ya rasu ne a wani asibitin sojoji a Paris a shekara ta 2004, bayan da kwatsam ya soma ciwo a fadar shugaban kasa a Ramallah.

Karin bayani