Masu sankarar huhu a Beijing sun karu

Inda ake kira Cancer Village a China
Image caption Inda ake kira Cancer Village a China

Yawan masu fama da kansar huhu a babban birnin kasar China, watau Beijing, yayi matukar karuwa a shekaru goman da suka wuce.

Hukumomin Chinar sun fitar da alkalumman ne, a daidai lokacin da ake cigaba da nuna damuwa a kasar, a kan cututuka masu alaka da gurbatar yanayi.

A cewar jami'an lafiya a birnin na Beijing, akalla yawan masu fama da kansar huhun ya karu da kashi hamsin cikin dari, idan an kwatanta da shekaru goman da suka gabata. Suka ce, shan taba shine babban dalilin da ya janyo hakan - ko da yake kuma sun yarda cewa, gurbatar yanayi shi ma yana taka rawa.

Mahukuntan Chinar dai basu yi wani bayani ba a kan abinda ya sa jama'a da yawa haka ke kara kamuwa da sankakar huhun ba.