Da sauran rina a kaba kan nukiliyar Iran

Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran
Image caption Tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran

Ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, wanda ke wakiltar kasar tasa a tattaunawar da ake yi a Geneva kan shirin Iran na nukiliya, ya ce har yanzu kawunan masu sasantawar a rarrabe suke.

A cewar Laurent Fabius, Iran ta shure bukatun da aka gabatar mata na ta daina sarrafa uranium a wata tasha, sannan kuma ta yarda a rage karfin uranium din da tuni ta sarrafa, ta yadda ba zata iya yin amfani da shi wajen kera bam din nukiliya ba.

Ya ce, an dan sami cigaba, amma a halin yanzu ba zai iya tabbatar da cewa za a kitse maganar ba.

Sai dai mataimakin ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araqchi, ya dage a kan cewa za a yita ta kare a yau din nan.

Idan kwa ba haka ba in ji shi, to sai a nan gaba za a tsayar da wani lokaci na cigaba da tattaunawar.