Mutane dubu 10 sun mutu a guguwar Philipphines

Image caption Jami'an birnin sun ce suna kokarin su raba kayan agaji sai dai mutane na wawasar kayyakin jama'a wurare masu yawa.

Jami'ai a kasar Philippines sun ce yanzu kimanin mutane dubu goma ne suke fargabar sun mutu a lardi guda kacal lokacinda mahaukaciyar guguwa da ruwan sama mai karfi suka yi kaca-kaca da tsibirrai da dama da ke tsakiyar kasar a ranar jumma'a.

Babban Sufurtandan 'yan sandan lardin na Leyte Elmer Soria yace gwamnan Lardin ne yayi masa bayani da safiyar Lahadi cewa akwai kusan mutane dubu goma da suka mutu a tsibirin galibinsu saboda nutsewa a ruwa ko rushewar gine-gine.

Babban jami'in 'yan sandan na Lardin ya ce an samu sabbin alkaluman ne daga rahotannin dake fitowa daga jami'an Kauyukkan dake yankin da abin ya shafa.

Magajin garin birnin Tacloban babban birnin lardin, Tescon Lim, ya ce wadanda suka mutu a garin kawai zasu kai dubu daya.

Karin bayani