Guguwa ta hallaka mutane a Philippines

Barnar mahaukaciyar guguwar Haiyan
Image caption Barnar mahaukaciyar guguwar Haiyan

A Philippines ana fargabar daruruwan mutane sun hallaka bayan da mahaukaciyar guguwar Haiyan mai tafe da ruwa ta kada a kasar a jiya Juma'a.

Sakataren kungiyar agajin Red Cross reshen Philippines din ya shaida wa BBC cewar, su na duba rahotannin da ke cewa, an ga gawarwakin mutane dayawa a cikin ruwa, a garin Tacloban na tsibirin Leyte.

Kungiyar Red Cross din ta kiyasta cewa, mai yiwuwa wadanda suka hallakar a Tacloban zasu kai dubu daya.

A wani lardin kuma an ga gawarwakin mutane dari biyu in ji kungiyar.

Tuni dai sojoji suka fara aikin ceto, to amma ruwa ya mamaye hanyoyi da dama kuma hanyoyin sadarwa a yawancin yankunan tsakiyar kasar ta Philippines sun lalace.

Mai yiwuwa sai nan da kwanaki masu yawa za a san ainihin munin barnar da guguwar ta haddasa.

A Vietnam hukumomi sun soma kwashe mutane fiye da dubu dari yayin da mahaukaciyar guguwar ta Haiyan mai dauke da ruwa ta doshi kasar.

Gobe ake zaton guguwar za ta isa kasar.