An kashe mutane a rikicin jihar Benue

Jami'an tsaron Najeriya
Image caption Jami'an tsaron Najeriya

A Najeriya 'yan bindiga sun kai hari a kauyuka da dama a jahar Benue, inda suka hallaka akalla mutane shidda, tare da kona gidaje masu yawa.

A cewar 'yan sanda, Fulani makiyaya ne suka kai hare-haren.

Kafofin yada labarai a jahar Benuen sun ce, yawan mutanen da suka mutun ya haura talatin, amma a hira da BBC, DSP Daniel Ezialla ya ce su aiya saninsu mutane shidda ne suka tabbbatar da mutuwarsu.

Ana jin tashin hankalin ya barke ne tsakanin makiyayan da manoma 'yan kabilar Tivi, a kan batun mallakar filaye da wuraren kiwo.