Birnin Tokyo ya girgiza

Image caption Girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 7:28 agogon kasar.

Wata girgizar kasa mai karfin awo 5.5 ta afkawa yankin gabascin Japan da ya kunshi har da babban birnin kasar, Tokyo, da safiyar Lahadi.

Ya zuwa yanzu ba a samu bayanin da ke nuna irin barnar da ta yi ba, kuma babu wata barazana daga igiyar teku ta Tsunami.

Girgizar kasar ta faro ne daga jahar Ibaraki da ke arewa-maso-gabascin birnin na Tokyo.

An dai dakatar da shawagin jiragen kasan nan masu gudu kamar walkiya da ake kira ''bullet trains'' na tsakanin Tokyo da arewacin Japan na dan wani lokaci bayan faruwar lamarin.

Karin bayani