Ana tura kayan agaji Philippines

Image caption Kasashen duniya na tara kayan agaji zuwa Philippines

Ana ci gaba da tara kayan agaji na kasa da kasa mai tarin yawa a kasar Philippines inda lamarin ya shafi mutane fiye da miliyan hudu.

Guguwar mai suna Haiyan, ta haifar da bala'i a yankunan tsakiyar kasar.

An yi amannar cewa mutane sama da dubu goma sun rasa rayukansu.

Dakarun sojin kasar Philippines na daukar tawagar masu kai agajin gaggawa zuwa wauraren da lamarin yafi kamari.

Karin bayani