Jami'an tsaro sun yi arangama da baki a Riyadh

Baki ma'aikata a Saudiyya
Image caption Baki ma'aikata sun yi arangama da jami'an tsaro a Saudiyya

'Yan Sanda a kasar Saudiyya sun yi arangama da baki 'yan kasar waje dake aiki cikin kasar wadanda ke zanga-zanga a wani yanki da ya kunshi talakkawa dake Riyadh babban birnin kasar.

Wata sanarwar 'yan sanda ta ce an kashe mutane biyu. An kame daruruwan masu zanga-zangar. Wasu hotunan video da aka saka a shafukkan sada zumunta na yanar-gizo sun nuna jami'an tsaron suna korar mutanen da kulake.

Tashe-tashen hankulan sun fara afkuwa ne kimanin mako guda bayan da hukumomin Saudiyyar suka fara daukar matakan kaame baaki 'yan kasar waje wadanda suka karya sharuddan iznin zamansu da takardun iznin aiki cikin kasar.

Daruruwan dubban mutane ne daga akasari Afrika da Asiya ke zaune cikin kasar ta Saudiyya ba tare da izni ba, wasun su ma suna tfaka ayyukan assha.

Karin bayani