An kama 'Yan Najeriya masu safarar mata a Spain

Kayan da 'yan sandan Spain suka kwace
Image caption Kayan da 'yan sandan Spain suka kwace

'Yan sandan kasar Spain sun kama wasu 'yan Nijeriya su ashirin da biyar, wadanda suka ce suna fataucin mata daga Nijeriyar, suna tilasta masu aikin karuwanci a kasar ta Spain ko a wasu kasashen Turai.

A wani bangare na aikin samamen , 'yan sandan sun kwace motoci casa'in da hudu a Madrid, da wasu karin ashirin da shidda a tashar jiragen ruwa ta Valencia.

Bisa dukkan alamu gungun mutanen na shakare manyan motocin da giya ne, da kuma akwatunan talabijin, amma sai su like motocin domin boye kayan dake ciki.

'Yan sanda sun gano kayayyakin da aka boye na kimanin euro miliyan biyar cikin motocin.

Ana kuma zargin gungun mutanen da aikata zamba da intanet, ta hanyar amfani da katunan bankin da suka sata.