An cimma yarjejeniya kan nukiliyar Iran

Image caption Shugaba Hassan Rouhani

Iran ta cimma yarjejeniya da hukumar kula da makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya IAEA a game da shirinta na nukiliya bayan tsaikon da aka samu na watanni.

Yarjejeniyar ta zayyana jadawalin fahimtar juna a kokarin rage damuwar da ake da ita game da shirin nukiliyar Iran din a baya.

Hakan ya share fage ga masu bincike su sami kaiwa ga muhimman tashoshi biyu na nukiliyar ba tare da shamaki ba.

Da yake jawabi ga 'yan jarida a Vienna kafin ya wuce Tehran, shugaban hukumar ta IAEA Yukia Amano ya baiyana yarjejejniya a matsayin matakin farko na cigaba.

"kamar yadda ku ka sani Iran ta gabatar da sabbin shawarwari a watan da ya gabata, wannan ya kunshi matakai na zahiri na karfafa fahimtar juna da tattaunawa, mun kuma kudiri aniyar cigaba akan wannan", in ji Amano.

Karin bayani