An harbe wani Ministan Iran har lahira

Shugaban Iran
Image caption Wani dan bindiga ya harbe Ministan Iran

An harbe wani Minista na gwamnatin Iran har lahira a Tehran babban birnin kasar.

Mataimakin Ministan na Masana'antu, ma'adinai da kasuwanci Safdar Rahmat Abadi an ce yana tuka motarsa ne a lokacinda ya ratsa ta dandalin Tehran dake gabashin birnin lokacinda aka harbe shi.

Rundunar 'yan sandan kasar ta Iran sun ce an samu fankon da ake duura harsahi cikinsa guda biyu a cikin motarsa, abinda ya nuna cewar mutumen da ya kashe shi yana cikin motar ne.

Ba a dai san wanda ya yi wannan aika-aikar ba.