Amurka za ta kai gudummawa Philippines

Image caption Gwamnatin Burtaniya ma dai ta ce sojojin ta kusa dari biyu za a tura domin sa hannu cikin aikin na ba da agaji.

Amurka za ta tura wani katafaren jirgin ruwa na yaki dake dakon jiragen sama don taimaka ma ayyukan agaji a kasar Phillipines a sakamakon barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta yi inda ta hallaka dubban mutane.

Wata sanarwa da Mai'aikatar Tsaron Amurkar ta Pentagon ta fitar ta ce Sakateren Tsaron Amurkar Chuck Hagel ya umarci matuka katafaren jirgin na dako jirage ake yiwa lakabi da USS George Washington da kuma wasu jiragen sojin ruwan Amurka da suyi gudu bakin iyawarsu domin su ga sun isa a Jamhuriyar Philippines

Kasashe da dama dai na kara yunkurowa don taimakawa ga ayyukan agajin na gaggawa.

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki moon ya bayyana hotunan da aka nuna a talabijin na bannar da guguwar ta yi a matsayin wani abin ban tausayi tare da yin kira ga kasashen duniya su hada kai wajen taimaka ma dubban mutanen da bala'in ya afka ma wa.

Karin bayani