Iska mai karfi ta kashe mutane 100 Somalia

Image caption Shugaban Puntland, Abdulrahman Farole

Shugaban kasar yankin Puntland na Somalia mai kwarya-kwaryar cin gashin kai Abdulrahman Farole ya shaidawa BBC cewa mutane kusan 100 sun rasu a yankin, bayan aukuwar iska mai karfi hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya a karshen mako.

Shugaban ya ce dubban dabbobi sun mutu kuma daruruwan gidaje sun ruguje.

Mr Farole ya ce hanyoyin isa ga yankunan da abin ya shafa a garin Eyl sun katse kuma a yanzu haka suna kokarin yadda za su kaiwa jama'a taimakon abinci da suka hada da dabino da kuma biskit ta jirgin sama.

An ruwaito cewa masunta da dama sun bace har yanzu ba'a gano su ba.

Karin bayani