'Yan gudun hijirar Somalia zasu bar Kenya

Image caption Somaliyawan sun nemi mafaka a Kenya ne don gujewa yaki da kuma yunwa.

'Yan gudun hijirar Somalia dake zaune a Kenya dubu 500 ne za a mayar dasu kasarsu bayan Hukumar Kula da 'yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta sa hannu kan wata yarjejeniya tsakaninta da gwamnatocin kasashen biyu ranar Lahadi.

A karkashin wannan yarjejeniyar, za a mayar da Somaliyawan ne bisa radin kansu a cikin shekaru uku masu zuwa.

Somaliyawa fiye da miliyan daya ne yanzu haka ke tsugune a sansanonin 'yan gudun hijira na Dadaab da Kakuma da ke arewacin Kenya.

Gwamnatin Kenya dai ta damu da barazanar da 'yan ta'adda ke yi mata, sakamakon harin da 'yan bindiga daga Somaliya suka kai kan shagon Westgate da ke birnin Nairobi a watan Satumba.

Karin bayani