'Yan adawa a Syria sun sa sharuddan zuwa taron Geneva

'Yan tawayen Syria
Image caption 'Yan tawayen Syria sun ce za su halarci taron zaman lafiya amma da sharudda

Kungiyar 'yan adawa a kasar Syria watau Syria National Coalition ta ce za ta halarci wani taro da nufin kawo karshen yaakin basasar da ake yi a kasar, muddin aka cimma wasu sharudda gabanin tattaunawar.

Kungiyar ta yi kiran a bayar da tabbatacin kyale kungiyoyin ba da agaji su shiga yankunan da aka mamaye da kuma sakin fursunonin siyasa.

Har ila yau kuma kungiyar tace duk wani taro da za a yi lallai ne ya haifar da sauyin Shugabanci.

Gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad ta yi watsi da duk wasu sharudda da aka gindaya game da taron da za a yi a Geneva - wanda kasashe irinsu Amurka da Rasha ke kokarin shiryawa nan gaba a cikin wannan watan.