An zabi sabon shugaban Majalisar Taraba

  • 11 Nuwamba 2013
Akwai takun saka a majalisar dokokin jihar Taraba

Majalisar Dokokin Jihar Taraba, a arewa maso gabashin Najeriya ta zabi sabon kakakinta, mako daya cif-cif bayan mutuwar kakakin majalisar, Mista Haruna Tsokwa, sakamakon rashin lafiya.

Wanda 'yan majalisar suka zaba a matsayin sabon kakakin ba tare da hamayya ba, shi ne Honourable Josiah Sabo Kyante.

Sabon kakakin na daga cikin 'yan majalisar 16 da a watannin baya suka goyi bayan wani kuduri da ya baiwa mukaddashin gwamnan jihar, Alhaji Garba Umar, damar ci gaba da jan ragamar jihar, zuwa lokacin da wa-la-Allah gwamnan jihar, Mista Danbaba Suntai, zai samu lafiya.

A baya-bayan nan dai jihar ta Taraba ta yi ta shiga kanun labarai sakamakon dambarwar siyasarta, musamman bayan komawa da gwamnan jihar Danbaba Suntai gida daga kasashen waje inda aka kai shi jinyar raunukan da ya samu a hadarin jirgin sama.

Karin bayani