Za'a biya mata masu shayarwa £200

Masana na shawartar mata su shayar da 'ya'yansu nono zalla tsawon watanni shida.
Image caption Masana na shawartar mata su shayar da 'ya'yansu nono zalla tsawon watanni shida.

Za'a fara biyan iyaye mata a Britaniya £200 domin su shayar da 'ya'yansu nono.

Gwamnatin Britaniya tare da masu binciken kiwon lafiya ne za su daukin nauyin shirin a yankunan talakawa da ke kudancin Yorkshire da Derbyshire.

Za'a fara shirin ne da mata 130 masu haihuwa daga yanzu zuwa watan Maris.

Idan shirin ya yi nasara za'a fadada shi zuwa sauran sassan kasar a badi.

A baya dai hukumar kiwon lafiya ta Birtaniya ta yi amfani da kudi wurin karfafa gwiwar mutane su bar shan taba sigari da kuma rage kiba.

karo na farko

Sai dai wannan ne karo na farko da za'a gwada amfani da kudi don bunkasa shayar da jarirai nonon uwa.

A karkashin tsarin, za'a baiwa iyaye mata a Sheffield da Chesterfield takardun da za su iya amfani da su wurin yin cefane a kantuna.

An zabi yankunan ne saboda karancin shayar da nonon da suke fama da shi. Mace daya cikin hudu ce kawai a yankin kan shayar da 'ya'yanta nono tsawon makonni shida zuwa takwas, sabanin sauran sassan kasar da kusan rabin matan kan shayar da 'ya'yansu tsawon makonni takwas.

Domin samun kyautar £200, za'a bukaci matan da su shayar da 'ya'yansu har zuwa watanni shida. Wadanda za su yi shayarwar watanni shida kuma za su sami £120.

Masu tsara shirin dai sun ce shayar da jarirai nonon uwa na kare su daga ciwon ciki da kirji tare kuma da kara musu kokari a makaranta.

Dr Clare Relton ta jami'ar Sheffield, wacce ke jagorantar shirin ta ce ta na fatan salalar kudin za ta haifar da dabi'ar shayar da jarirai nonon.

Sai dai Janet Fyle, ta kwalejin unguzomomi ta Birtaniya na tababar nasarar shirin.

"Shayar da jarirai nono ba abu ne da ya kamata a gina shi kan harsashin samun kudi ba. Kamata ya yi a ce wani abu ne da iyaye mata ke yi domin kare lafiyar 'ya'yansu."

Ta ce za'a iya bunkasa shayar da nonon uwa ne kawai ta hanyar samar da isassun ma'aikata da za su bada cikakkiyar kulawa da shawarwari ga iyaye mata bayan haihuwa.