An bayyana sabbin sauye-sauye a China

Image caption Inda shugabannin China su kayi taro

Shugabanni a China sun kamalla wani taron koli cikin sirri idan suka bayyana wasu daga cikin sauye-sauyen da za su gudunar cikin shekaru goma masu zuwa.

Sanarwar da aka fitar, ta nuna cewar za a bar kasuwanni su ci gashin kansu.

Jami'an jam'iyyar kwaminisanci sun yi gargadin cewar sauyin zai kasance da girman da ba a taba gani ba.

Za a kafa wani sabon kwamiti da zai lura da tsaron cikin gida domin magance boren jama'a sannan za 'a baiwa manoma karin iko a kan gonakinsu.

Karin bayani