Gwamnatin Masar ta dage dokar ta baci

Dokar ta baci a Masar
Image caption Dokar ta baci a Masar

Gwamnatin Masar ta dage dokar ta bacin da ta sanya watanni uku da suka wuce sakamakon tashin hankalin da ya biyo bayan hambarar da shugaban kasar na jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi, Mohammed Morsi.

Matakin dage dokar ta bacin ya biyo bayan yanke hukuncin da kotu ta yi.

Wani wakilin BBC yac e wannan baya nufin za'a sami karin yancin walwala akan tituna.

Za'a tura jami'an tsaro zuwa manyan birane domin tabbatar da doka da oda.

Ana kuma sa ran gwamnati za ta fito da wata sabuwar doka a wannnan makon ta haramta gangamin zanga zanga.