Jami'an Masar sun hana dan kwallo wasa

Ahmed Abdul Zaher dan kwallon Masar
Image caption Dan kwallon Masar da aka hana shiga gasar kwallo saboda ya nuna wata alama ta goyon bayan Mohammed Morsi

An dakatar da daya daga cikin manyan 'yan kwallon kasar Masar daga shiga gasar kwallon kafa ta kasashen duniya da za a yi cikin wata mai zuwa bayan ya nuna wata alama ta nuna goyon baya ga hambararren Shugaban kasar dan kishin Islama Mohammed Morsi lokacinda ake wasan karshe na zakarun kwallon kafa na nahiyar Afrika.

Ahmed Abdul Zaher ya daga hannunsa ne ya nuna yatsu hudu - alamar da aka fi sani da Rabaa - bayan ya ci kwallon lokacinda ake gasar a ranar lahadi.

Ahmed din dai ya ce ya yi hakan ne don tunawa da dukkan mutanen da suka rasa rayukkansu a lokacin rikicin siyasar kasar - koda kuwa 'yan sanda ne ko farar hula.

Ministan wasanni na kasar ta Masar ya bayyana abinda dan wasan ya yi a matsayin wata babbar rashin kunya.

Karin bayani