Datse bututun mai na barazana ga Libya

'Yan bindiga na datse bututun mai a Libya
Image caption 'Yan bindiga na datse bututun mai a Libya

Asusun bada lamuni na duniya ya ce tattalin arzikin kasar Libya zai ragu da kimanin kashi biyar cikin 100 a wannan shekarar saboda katsewar da ake samu na tono mai a dalilin masu bore da kan toshe cibiyoyin man.

Mutane da dama a yankin gabashin kasar mai arzikin mai inda aka faro guguwar juyin juya hali suna jin cewa gwamnatin tarayya a birnin Tripoli ta yi watsi da su inda sau da dama suka rika katse tunkuda man.

A ranar Lahadi wata kungiya da ke rajin neman 'yancin kai a gabashin kasar ta kafa wani kamfani da zai rika sayar da man a cibiyoyin dake karkashin ikonta.

Pirai ministan Libyan yace kasar na fuskantar gibin kasafin kudi saboda an dakatar da kusan kashi 60 cikin 100 na aikin hakar man.