MASSOB ta ce an kashe mambobinta

Peter Obi, Gwamnan jahar Anambra
Image caption Peter Obi, Gwamnan jahar Anambra

A Najeriya kungiyar MASSOB mai fafutukar tabbatar da kafuwar jamhuriyyar Biafra ta zargi jami'an tsaro da kashe mata mutane hudu.

Kungiyar ta kuma ce, wasu mambobinta fiye da tamanin sun sami munanan raunuka a birnin kasuwancin Onitsha da ke jihar Anambra.

MASSOB ta dora alhakin aukuwar hakan ne kan jam'iyyar APGA mai mulkin jahar.

Ta ce jam'iyyar ta APGA na kuntata mata ne don ta ki kawo goyon bayanta da zaben gwamnan jihar ta Anambra da za a gudanar a karshen makon nan.

Sai dai rundunar 'yan sandan jihar ta Anambra da bangaren gwamnan jihar duk sun musanta zargin na MASSOB.