PDP: Oyinlola ya maida martani

Alamar jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria
Image caption Alamar jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria

Tsohon sakataren PDP mai mulkin Nigeria, Olagunsoye Oyinlola wanda kotu ta tabbatar masa da mukaminsa a makon jiya ya mai da martani kan dakatar da shi da jam'iyyar ta yi.

Mr. Olagunsoye Oyinlola yace dakatarwar ta sabawa doka tunda babu wanda ya tuntube shi don ya kare kansa daga zargin da ake masa kafin ace an dakatar da shi.

Ya kuma ce idan da gaske ne don me mahukuntan PDP suka kasa dakatar da gwamnoni da 'yan majalisu na jam'iyyar da suka balle suka kafa tsagin sabuwar PDP.

A nasa martanin, Ambasada Ibrahim Kazaure, daya daga cikin wadanda aka dakatar tare da Oyinlola ya ce babu mamaki don shugabannin PDP sun karya doka don kuwa halinsu ne.

Ambasada Kazaure ya ce dama PDP ba so take a sasanta rikicin da ke cikinta kuma su sun daura aniyar rigima da PDP "har zuwa yaumut tanadi."