Al'ummar Philippines na tsaka mai wuya

Image caption Kasashen duniya na tallafawa Philippines

Ana tsuga ruwan sama kamar da bakin kwarya a Tacloban na Philippine, daya daga cikin garuruwan da mahaukaciyar guguwar Haiyan ta fi yiwa barna.

Mamakon ruwan saman na kara uzzurawa dubunnan mutanen da ke rayuwa cikin kufan gidajensu.

Abinci da ruwan sha sun yi karanci har ta kai mutane na tace ruwan kwata da rigunansu su na sha.

Jiragen sojin Philippine da Amurka na kai agaji garin sai dai babu wata alamar agajin na isa ga mabukata.

'Barna mafi tsanani'

Wuraren da mahaukaciyar guguwar tafi barna dai sun hada da tsibiran Leyte da Samar na Philippine sai dai ana samun bayanan barnar a wasu sassan.

Wakilin BBC da ya ziyarci tsibirin Cebu ya tarar da gidajen kauyukan yankin a rushe, gadoji sun karye, sannan hanyoyi sun lalace.

Mazauna birnin Cebu kansa, inda mahaukaciyar guguwar ba ta yi barna sosai ba, na raba agaji da kansu, amma babu wata alamar mahukunta ko kungiyoyin agaji na bada wani tallafi.