Wani mawaki dan Iran ya kashe takwarorinsa

Majalisar dokoki da Shugaba Rouhani
Image caption An harbe wasu mawakan Iran mazauna Amurka har lahira

An harbe wasu mawaka hudu 'yan kasar Iran dake zaune birnin New York har lahira.

'Yan sanda sun ce daya daga cikinsu Ali Akbar Mahammad Rafie ne ya harbi wasu mutanen ukku da suka hada da biyu daga cikin 'yan kungiyar mawakan da ake kira Yellow Dogs - kafin ya juya bindigar ya kashe kansa.

Lamarin ya afku ne a wani gida dake Brooklyn. Jami'ai sun ce an raunata wani mutumin na hudu a lokacinda ake harbe-harben, amma dai yanzu haka yana cikin hayyacinsa.

Manajan kungiyar mawakan ta Yellow Dogs ya ce, maharin, ya shafe watanni baa ya magana da sauran takwarorinsa saboda wata rashin jituwa dake tsakaninsu.

Karin bayani