Noman ganyen taba ya karu a Afghanistan

Noman ganyayyaki masu sa maye a Afghanistan
Image caption Noman ganyayyaki masu sa maye a Afghanistan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce noman ganyayyakin da ake sarrafawa ana miyagun kwayoyi da su ya karu ainun har ya kai yawan da bai taba kaiwa ba a shekarar nan.

Tan dubu biyar da rabi na Opium da aka noma a kasar a bana ya zarta na shekara ta 2007.

Kafin yanzun ba a taba noma wanda ya kai yawansa ba, kuma za a iya samar da hodar iblis ta heroin da Opium din da yawanta zai dara abinda ake bukata a duniya.

Babban jami'in ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin miyagun kwayoyi da manyan laifuka a Kabul, Jean-Luc Lemahieu, ya ce da alamu noman ya sake karuwa a shekara mai zuwa, yayin da ake fargabar shiga yanayi na rashin tabbas a kasar, saboda janyewar galibin sojojin kasashen waje, da kuma zaben shugaban kasar ta Afghanistan da za a yi.

Ya ce nauyi ya hau kan kasashen duniya na taimaka wa kasar ta Afghanistan.